Saudiyya: Mata zasu samu guraben aiki

Hakkin mallakar hoto Getty

Ma'aikatar ƙwadago ta Saudi Arabia ta bada umarnin cewa, dole kowanne kamfani ya ɗau ma'aikata mata aƙalla goma.

Sabon sauyi ga dokokin aikin kwadago sun nuna cewa, mata zasu rika aiki ne daga karfe 6:00 na safe zuwa karfe 5:00 na yamma.

Hukumomin Saudiyyar sun buƙaci kamfanoni masu zaman kansu da ma'aikatun gwamnati soma aiwatar da waɗannan sauye-sauye.

Jaridar Arab News ta ce, ma'aikatar ƙwadagon ta ce, ana ƙoƙarin ganin kamfanoni suna daukar ma'aikata mata a kowanne bangare.

Khalid Aba Khalil jami'i a ma'aikatar yada labarai ya ce, yanzu kamfanoni suna kawo sauye-sauye da za su sauƙaƙawa mata yin aikin a kamfanoni.

A Saudiyya an hana mata yin ire-iren ayyuka 24, kuma duk aikin da mata zasu yi ba zai wuce na awa 8 ba a kowacce rana.