Wani gini da ya rufta ya kashe mutane 3 a Kebbi

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Rahotanni daga jihar Kebbi sun ce mutane 3 suka rasu ya yinda 4 sun ji raunuka bayan da wani bangare na gidan da amajirai suke zaune ya rufta.

Bayanai suce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar a garin Argungu da ke jihar Kebbin lokacinda almajirai suke karatu.

Malamin tsangayar Sani Abdullahi ya shaidawa BBC cewa ruwan sama tare da iska mai karfi da aka yi su ne suka sa wani bangare na ginin ya rufta.

Tuni aka yi janaizar mutanen da suka rasu.