Sojoji sun gano rumbun abincin BH

Sojojin Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Najeriya da ke fagen daga a Borno

Rundunar sojin kasa ta Najeriya, ta ce gano wurin da mayakan Boko Haram suke adana abinci domin kaucema bacin rana a karamar hukumar Bama da ke jihar Borno.

Ta ce dakarunta sun bankado babban ramin ne a farmakin da suka kai wa kauyukan Biggoro da Warpaya da Aura da kuma arewacin kumshe.

Kakakin rundunar sojin kasa kanal Usman Sani Kukasheka ya ce sojoji sun kashe mayakan kungiyar Boko haram biyu kuma sun kubatar da yara kanana biyu daga hannunsu.

Ya kuma ce sojoji sun gano cewa mayakan Boko Haram na hawan saman bushiya domin su hango ko za a kawo ma su farmaki.