Farashin fetur ya sake faduwa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An gaza rage yawan man da ake sayarwa ne saboda rigima tsakanin Iran da Saudiyya.

Farashin mai ya faɗi a bayan taron ƙasashe masu arzikin man ya gaza rage yawan man da suke haƙowa, domin farfado da farashin man.

Cikin 'yan awoyi, farashin man ya fadi da kashi biyar cikin dari a kasuwar duniya.

Tattaunawar ta fuskanci koma-baya ne saboda batun kace-nace da aka yi tsakanin Saudiyya da Iran.

Saudiyya ta ce ba za ta rage yawan man da take haƙowa ba sai Iran ma ta yarda ta yi hakan.

Amma Iran tana so ne ta sayar da mai sosai domin cin gajiyar janye mata takunkumin hana sayar da man da aka yi.

Ƙasashe masu arzikin mai sun yi fatan farfaɗo da farashi yayin taron.