Kasashen OPEC na taro a Doha

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Helkwatar kungiyar OPEC da ke birnin Geneva

Kasashe masu arzikin man fetur sun soma taro a Doha, babban birnin Qatar domin tattauna yadda zasu daidaita akan yawan man da zasu rage da suke fitarwa domin farashi ya inganta.

Faduwar farashin gangar man fetur, ta shafi tattalin arzikn da dama daga kasashen da ke halatar taron.

Yanzu haka dai ana sayar da danyen mai a kasuwar duniya akan rabin farashin da aka sayar da shi shekaru biyu da suka gabata.

Saudiya da Rasha na fatan matakin zai sa a samu raguwa a yawan man fetur din da ake fitar domin farashin ya inganta.

Sai dai kasar Iran wadda ta ke da dimbin arzikin man ta ce ba za ta rage yawan man fetur din da ta ke fitarwa ba kuma zata kauracewa taron.