Fasa bututun mai ya ta'azzara rashin lantarki

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

A Najeriya ga alama matsalar tsananin karancin wutar lantarki da ake fama da ita yanzu haka a kasar za ta dore har zuwa karshen watan gobe.

Gwamnatin kasar dai ta ce ana samun karancin wutar ne sakamakon lalata wasu manyan bututan man gas da ke samar da kashi arba'in cikin dari na yawan gas din da tashoshin samar da wutar lantarki ke amfani da shi.

Yayin da a yanzu ofishin mataimakin shugaban kasar ya ambato kamfanin mai na shell na cewar gyaran bututan zai kai har karshen watan Mayu.

Matsalar karancin man fetur da wutar lantarki na cikin matsalolin da ke addabar kasar.

Image caption Rashin wutar lantarki na daya daga cikin matsalolin da ke addabar Najeriya, inda ya ke janyo wa tattalin arzikin kasar koma baya.