Yadda ake satar jarrabawa a Ghana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yawancin 'yan Ghana na fatan za a samu ci gaba a tsarin makarantu saboda su samu ayyuka masu inganci.

A ci gaba da jerin wasikun mu daga 'yan jaridar Afrika, marubuciyar nan Elizabeth Ohene ta duba hanyoyin ban mamaki da dalibai ke bi suna satar amsa a lokacin jarabawa a Ghana.

Yayin da duniya ta sanya batun takardun Panama gaba, a kasar Ghana an kwarmata yadda ake satar amsa.

Sun shiga wani hali da ya kunyata kasar baki daya, inda a bana, kamar sauran shekaru da suka gabata, aka samu rahotannin da ke cewa an samu tambayoyin jarrabawar makarantar sakandare, da ake cewa jarrabawar West African Senior School Certificate.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An samu satar amsa ta kafofin sada zumunta.

Ana shirin gudanar da jarrabawa da safe, sai wata jaridar kasar ta fitar da rahoton cewa tambayoyin darussa guda uku, da Ingilishi da Kimiyya da Karatun yanayin al'umma watau Social Studies, sun riga sun fito, inda wasu daliban suka riga suka samu ta kafofin sada zumunta tun karfe hudu na asuba.

Lokaci dai ya canza, ganin yadda ake samun hotunan rubuce-rubuce da dalibai ke yi a cinyoyinsu, wadanda aka gano cewa amsoshin tambayoyin da suke kyautata zaton za a tambaye su ne a jarrabawar.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba John Mahama ya bayyana bacin ransa ga jami'an hukumar shirya jarabawar yankin, ganin yadda suka bari har tambayoyin suka fito.

Kamar dai yadda ake zato, abin ya janyo cece-kuce sosai daga al'ummar Ghana, har ga shugaban kasar ma John Mahama, wanda ya bayyana bacin ransa ga sakacin hukumar shirya jarrabawa ta Afrika ta yamma, wajen kare martabar jarrabawa a kasar.

'Takardu maras inganci'

Shugaban babban ofishin hukumar shirya jarrabawa ta Afrika ta yamma na kasa dai ya bayar muhimmin dalili, inda ya ce abin da ya faru, ba wai kwarmata bayani kan jarrabawa za a ce ba, sai dai a ce daliban sun samu ilimin tambayoyin kan su fito.

Bayanin dai a takaice na nufin, an yi satar amsoshi ne idan tambayoyin sun fito kwanaki kafin jarrabawar, amma tun da sun fito ne sa'o'i kalilan kafin jarrabawar, to ilimin jarrabawar suka samu.

Abin mamaki shi ne yadda yawancin mutane suka fi damuwa da takardunsu, ina suke fargabar kar su zamo ba su da amfani, da rashin kima a kasashen da 'yan Ghanan ke burin yin aiki a duniya, kamar Biritaniya da Amurka da Australia, da sauransu.

Ga alamu in dai a Ghana ne, rashin kimar takardun ba wata babbar matsala ce ba, tunda suna iya amfani da su wajen samun aiki a kasar.

Iyaye na biya

Ba Ghana ce kadai ke da makamancin wannan matsala ba, tun da rahotanni sun nuna cewa ana samun irin haka a Kenya da Zambia da Zimbabwe, da kasashen Afrika ta yamma da ke makwabtaka da Ghanan ma.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mutanen da ke burin shiga soja a Indiya na rubuta jarabawa tumbur babu kaya, domin tabbatar da cewa basu yi satar amsa ba.

Akwai rahotannin da ke cewa ana samun labaran satar amsa kafin jarrabawa a Indiya ma.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi zargin ana sayan takardun jarabawan ma a Ghana.

Akwai labaran da ke cewa iyaye na bai wa 'ya'yansu kudi domin sayen tambayoyi kafin jarrabawar ta fito da kuma wadanda ke cewa Malamai ma na yi wa daliban tayin tambayoyin jarrabawar.

Matsalar ta shafi rayuwar al'umma, inda yawancin ayyuka da ake gudanarwa a kasar ba su da muhimmanci, tunda galibin mutan garin ba su da ilimi da kwarewa, shi ya sa manyan jami'o'i ke samun matsala wajen gudanar da ayyukansu.