Me ya sa mata ke yin bilicin?

Image caption Mata sun ce suna bilicin ne domin su kara kyau

Wasu mata sun ce suna shafe-shafen man kara hasken fata ne saboda su kara kyau kuma maza su so su, yayin da wasu kuma ke ganin cewa shafe-shafen basa burge su.

Wata mata da take yin shafe-shafen da aka fi sani da bilicin ta ce ta fara yin sa ne saboda ta kara haske saboda ta ga hankalin akasarin maza a yanzu ya fi karkata ne a kan fararen mata.

Sai dai ita kuma wadda ba ta bilicin din, cewa ta yi ita tafi son launin fatarta a yadda ya ke wato baka, domin sam bilicin ba ya burgeta.

A halin da ake ciki dai a yanzu akwai mata wadanda ke canja kalar fatarsu ta hanyar shafe-shafen man da ke kara haske, inda zaka mace da baka kirin ce, amma da zarar ta fara shafa man bilicin sai ka ganta ta dawo kamar tsada saboda tsabar haske.

Aisha Shariff Baffa ta tattauna da wasu mata biyu--daya mai yin shafe-shafe, dayar kuma ba ta yi--don jin dalilan da suka sa ko wacce ta zabi ta zama yadda take, ga kuma yadda tattaunawar ta su ta kasance.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti