Sojoji sun fatattaki 'yan BH daga Kareto

Hakkin mallakar hoto AFP

Rundunar sojojin Najeriya ta ce dakarunta sun dakile harin da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai musu a a kauyen Kareto da ke jihar Borno.

Kakakin rundunar sojojin kasa ta Najeriya, Kanal Sani Kukasheka Usman, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya aikewa manema labarai, ya kara da cewa dakarunsu sun kashe 'yan kungiyar Boko Haram da dama.

A cewar sa, sojoji 22 ne suka samu rauni, kuma an kai su asibitin sojoji na Maiduguri domin yi musu magani.

Tun da fari dai, rundunar sojin Najeriya ta ce 'yan kungiyar Boko Haram sun kai hari kan dakarunta na Bataliya ta 113 da ke Kareto a arewacin jihar Borno.

Rahotanni daga jihar Bornon sun ce mayakan kungiyar Boko haram sun kai wa sojojin Najeriya harin kwanton-bauna a garin na Kareto da ke kusa da kan iyakar Najeriya da Nijar.

Kanar Sani Kukasheka Usman ya ce dakarun sun fafata da mayakan Boko Haram tun daga sanyin safiyar ranar Litinin.

Wata majiya a rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ce wasu sojoji sun rasa rayukansu, yayin da kuma wasu suka bata sakamakon harin.

Sai dai wani mazaunin yankin ya shaidawa BBC cewar sojojin Najeriya sun kashe mayakan kungiyar Boko Haram da dama kuma garin Kareto na karkashin ikon sojojin Najeriya.