An amince a tsige Shugabar Brazil

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu goyon bayan Rouseff sun nuna bacin ransu kan kuri'ar da aka kada.

Rikicin siyasa a Brazil na karuwa bayan majalisar wakilan kasar ta kada kuri'ar amincewa a ci gaba da yunkurin tsige shugabar kasar Dilma Rouseff.

Kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar dokokin sun amince da yunkurin tsige shugabar kasar.

Yanzu dai za a mika zarge-zargen da ake yi wa shugabar kasar ga majalisar dattawan kasar, wadda ake sa ran za ta dakatar da Shugaba Rouseff na tsahon watanni shida domin gudanar da bincike.

Amma jam'iyyar shugabar kasar, Workers' Party, ta zargi 'yan adawa da yunkurin yin juyin mulki a fakaice.

Ta kara da cewa za ta yi bakin kokarinta domin ganin ba a tsige shugabar kasar ba.

Nasarar da 'yan adawa suka samu gagarumin koma baya ne ga shugaba Dilma.