Nigeria: NLC na shirin fito-na-fito da sanatoci

Hakkin mallakar hoto b
Image caption Kungiyar NLC ta ce zata yi fito na fito da mambobin majalisar dattawa

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, ta ce za ta yi fito-na-fito da mambobin majalisar dattawan kasar idan har ba su mayar da motocin kawar da aka sa ya musu ba.

Kungiyar dai ta yi watsi da matakin da sanatocin suka dauka na karbar motocin kirar Toyota Land Cruiser guda 108 wadanda za a ba wa kowanne sanata daya, bayan kuma sun karbi bashin motoci a watan Augustan bara in ji kungiyar.

NLC ta cigaba da cewa wannan abin kunya ne,saboda kwamitocin majalisar da aka nada sun ce ba za su iya wasu ayyuka ba saboda babu kudi, amma kuma yanzu an ba su motoci sun karba.

Kungiyar ta ce su a matsayinsu na 'yan kasa suna ganin wannan abu sam bai dace ba, saboda an karawa motocin kudi, inda a da aka ce kowacce mota za a siyo ta a kan kudi naira miliyan 17, amma kuma sai gashi yanzu an kara zuwa naira miliyan 35.

Abin tambayar da 'yan Najeriya za su yi shi ne a ina aka samo wadannan makudan kudade bayan ba a amince da kasafin kudi ba? in ji NLC.

Kungiyar ta ce abin da kakakin majalisar dattawan Aliyu Sabi Abdullahi ya fake da shi ne, na cewa, wai masu bai wa shugaban kasa shawara na amfani da motoci kirar Jeep, to me ya sa sanatoci ba za su yi ba, shin ana so ne su tafi a kafa? Wannan magana kungiyar ta ce abin dariya ne kuma wasan yara ne.