Saudiyya za ta rage raɗaɗin janye tallafin fetur

Hakkin mallakar hoto AP

Gwamnatin Saudiyya ta ce tana daukar matakan rage raɗaɗin janye tallafi a wasu sassa na buƙatun yau da kullum.

Mataimakin Yerima mai jiran gado na Saudiyya, Muhammed bin Salman ne ya bayyana haka.

Ya kara da cewa gwamnati za ta dauki matakin ne ta hanyar samar da tallafi ga masara galihu, da kuma masu matsakaicin hali da suka dogara da tallafin da da gwamnati take samarwa.

Tallafin zai taimaka wa masu karamin ƙarfi wajen biyan kuɗin wutar lantarki, da man fetur da ruwan sha.

Janye tallafi a wasu fannoni ya soma aiki ne a Saudiyya a ƙoƙarin rage dogaro da kuɗin shiga daga man fetur.

Faɗuwar farashin man a kasuwar duniya ta sa Saudiyya tana ƙoƙarin rage dogaro da man.