Mutane 4 sun mutu a Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Reuters

Makaman roka da aka harbo daga Syria sun tsallaka kan iyakar kasar da Turkiyya, suka kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane 4.

Gwamnan yankin Kilis da ke Turkiyya, ya ce uku daga cikin su yara ne 'yan Syria.

Kamfanin dillancin labarai na Dogan a Turkiyyar, sun ce an harba akalla roka hudu daga wani yanki a Syria da ke karkashin ikon Kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulinci, watau IS.

A kwanan baya ne sojojin gwamnati Syria suka sake kwato wasu yankuna daga hannun mayakan IS, inda kungiyar sa ido da kare hakkin bil Adama a kasar wadda ke da mazauninta a Birtaniya ta ce sojojin shugaba Assad sun kwato fiye da rabin garin na al-Qaryatain sai dai kuma ana ci gaba da gwabza fada a wasu wuraren.