US: An yi doka kan hotunan batsa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gwamnan Utah, Gary Herbert yayin fito da kudiri kan hotunan batsa

Jihar Utah ta Amurka ta zartar da wani kudirin doka da ya ayyana hotunan batsa a matsayin abubuwan da ke da matukar haɗari a tsakanin al'umma.

Ita ce dai jihar farko da ta bayyana hakan a kafatanin jihohin Amurka.

Dokar dai ba ta haramta hotunan na batsa ba amma kuma ta nemi da ta yi rigakafi kan yawan kallon hotunan ba.

Dokar ta ce kallon hotunan batsa ga ƙananan yara, na lalata tunaninsu da tarbiyarsu.