Apple ya amince da dokokin bayar da bayanai

Hakkin mallakar hoto .
Image caption A baya dai kamfanin na Apple ya ki ba da hadin kai

Yanzu haka, ta bayyana cewa kamfanin Apple yana ba wa hukumomin Amurka hadin kai wajen samun bayanan masu amfani da wayoyin kamfanin na Apple.

Kididdiga daga kamfanin ta nuna cewa a 2015, Apple ya saki kaso 80 cikin dari na bayanan abokan huldarsa ga hukumomin Amurka, idan aka kwatanta da kaso 55 a Ingila.

Wani masanin harkar tsaro ya ce abin "bakin ciki ne" ga hukumomin tabbatar da anbi dokoki sau da kafa.

Kamfanin Apple ya saki rahoto ranar Litini kan bayanan da ya bayar tun daga 2013.

Apple ya buga lambobin bayanan wayoyin da hukumomin tsaro suka nema.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hukumomi suna zargin ana amfani da wayar iPhone wajen aikata laifuka.

Kamfanin ya kuma saki jerin bayanan da ma'aikatu suka nema da suka hada na iTunes da iCloud.

Cikin kasashe biyar da suka fi mikawa Apple bukatar neman bayanai, da suka kai 2,000 a kowace shekara, Amurka ce kawai kasar da take samun hadin kan kamfanin a kusan kodayaushe.

Kasar Singapore ce ta zamo kurar baya a kusan kowace shekara.

Kuma Amurka da Ingila ne suka kasance kasashen da suke neman bayanan mutane fiye da 300 a kowace shekara.