Borno: 'Yan gudun hijira na cin buhun shinkafa 1,800 kullum

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram sun lalata wurare da dama.

Gwamnan jihar Borno da ke Najeriya ya ce 'yan gudun hijirar da Boko Haram suka raba da gidajensu na cin buhun shinkafa 1800 a kullum.

Gwamna Kashim Shettima ya bayyana haka ne a wajen taro na farko wanda za a rika yi shekara-shekara kan sake gina jihar Borno wadda rikicin Boko Haram ya daidaita.

Kungiyar agaji ta AOA Global da gidauniyar Rhodes Trust da kuma gwamnatin jihar ta Borno ne suka dauki nauyin rika shirya tattaunawar, wadda ake yi a Abuja, babban birnin Najeriya.

Gwamnan jihar ta Borno ya kara da cewa "A yanzu haka da muke yin magana, muna fama da matsaloli na ciyar da 'yan gudun hijira. Sojoji sun yi nasarar ceto mutanen da 'yan Boko Haram suka rike. Don haka yanzu suna cin buhun shinkafa 1,800, wato Tirela uku a kullum".

Sai dai Gwamna Shettima ya ce 'yan gudun hijirar da ke sansanonin Ngala, wadanda suka kai 7,000, da kuma 60,000 da ke zaune a cikin garin basu da abinci sosai domin kuwa a kullum ana dafa musu shinkafa buhu 140.

Amma wasu 'yan gudun hijirar sun sha yin korafin cewa ba sa samun abinci.

Gwamna Shettima ya ce ya yi imanin cewar a yanzu an kawo karshen tayar da kayar bayan kungiyar ta Boko Haram wanda ya addabi jihohi masu yawa a arewacin kasar tsawon shekara shida.

Sai dai kalaman nasa na zuwa kwana guda bayan an yi wata mummunar ba-ta-kashi tsakanin sojojin Najeriya da mayakan Boko Haram a jihar ta Borno.