Ba zan yi murabus ba - Dilma Rouseff

Shugabar kasar Brazil Dilma Rouseff Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugabar kasar Brazil Dilma Rouseff

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff ta ce ba za tayi murabus ba, bayan da 'yan majalisar wakilan kasar suka kada kuri'ar amincewa da tsige ta.

Yayin da ta ke magana da kafafan yada labarai a Brasilia babban birnin kasar Ms Rousseff , ta ce ta fusata kan yadda masu adawa da ita ke jifanta da munanan kalamai a lokacin da yan majalisar wakilai ke kada kuri'a ranar Lahadi.

Ta jajirce a kan cewar ba ta aikata laifin cin hanci ba, kuma babu wasu dalilai na shari'a da za su sa a tsige ta.

Ana dai zargin Ms Rousseff da sauya kididdigar kasafin kudin kasar don taimakawa kan ta wajen sake tsayawa zabe a shekara ta 2014.

Nan da makonni masu zuwa ne ake sa ran gabatar da matakin tsige tan a majalisar dattawan kasar.