Garin da ban-daki ya kawo kyakkyawan fata

Hakkin mallakar hoto MaryAnn Ochota

Yaki da cin hanci da rashawa da talauci, su ne kalubalen da ke fuskantar Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, DRC, kuma ana kyautata zaton cewa shugaban kasar zai soke zaben da za a gudanar bana.

Amma duk da rashin daidaiton da hakan zai iya janyowa, Mary-Ann Ochota ta tarar da al'umma cike da kyakkyawan fata.

Bawili Amisi, wata mace ce siririya kuma kakkarfa, ga jijiyoyi duk sun fito a hannayenta, tana tuka tuwon garin kwaki, wanda 'yan Congo ke cewa fufu, abinci da yawanci ake ci a ko yaushe.

Ta kira iyalinta su ci abincin, su kuma basu bata lokaci ba suka hallara, ganin yadda yara ba sa wasa da harkar abinci a nan, kuma su ci suna godiya.

Labarin nan daga kudancin garin Kivu ne, wanda ke gabashin DRC, kuma a nan ne kauyen Bwalili, mai suna Mwandiga Trois, wanda ke yammacin tafkin Tanganyika ya ke.

Yanki ne gwanin ban sha'awa, dauke da tsaunuka da kasar noma mai daraja, inda ake girbi sau biyu na shekara.

Akwai rafi cike da kifaye, saboda haka bai kamata a yi kukan yunwa a nan ba.

A zahiri dai Congo na daya daga cikin kasashen da suka fi arziki a nahiyar Afrika, saboda arzikin noma da dubban ma'adanai da suke da shi.

Kasar tana da farin karfe da zinari da ma'adanin Uranium da Coltan wanda ake amfani da shi duk duniya wajen sarrafa wayoyin salula, amma kuma duk da wannan arziki, al'ummar Congo na fama da matsanancin talauci.

Shuwagabannin Congo sun dade suna almundahana da zalunci a kasar, inda shugaban kasar Joseph Kabila ke sauraren ra'ayoyin masu arziki su kadai, ba tare da mayar da hankali kan hadin kan kasa ba.

Hakan kuma na nufin kudaden kasar na tafiya ne kasashen waje ko kuma cikin aljihun wasu tsirarun jama'a, ganin yadda babu wata tsayayyar doka a kasar.

'Yanayin taka-ta-fisshe-ka'
Hakkin mallakar hoto MaryAnn Ochota

Labarin Bwalili tamkar labarin 'yan Congo ne baki daya.

A shekarar 1998 wasu 'yan bindiga suka dirar ma kauyensu, inda suka harbe mijinta har lahira.

Ta tsere zuwa kasar Tanzaniya da 'ya'yanta, inda ta shafe shekara goma a sansanin 'yan gudun hijira, bayan haka kuma tana cikin dubban mutanen da aka tilastawa komowa Congo a shekarar 2008.

Babu kwanciyar hankali a Congo, amma kuma Tanzaniya ta rufe sansanoninta.

"Rayuwar da wahala", in ji Bwalil tana murmushi, "Amma sai na soma noma kadan-kadan har na gina gida."

Ta nuno wani gini na laka da ke kusa, wanda aka yi wa taga da kwanon da ya yi tsatsa, kofar kuma rufe da dan tsumma mai kala.

Hakkin mallakar hoto MaryAnn Ochota

Bwalili ta kara da cewa, "Bani da karfin tona salga, ga shi bani da kudin sa wa a yi mani, ba mai taimaka mani da yara sai ni kadai."

'Yar Bwalili Ebinda, mai shekarar 14, na shiga daji domin yin ba-haya, kuma wata rana tana fitowa daga cikin dajin wasu maza suka tsare ta suka yi mata fyade.

Sanadiyyar haka ta samu ciki, ta haifi wata yarinya da a yanzu ke fama da tamowa.

A 'yan watannin da suka gabata ne kungiyoyin sa-ido na kasashen waje suka soma ayyukan taimako, wanda suka hada har da tona ban-dakuna a kauyukan kasar, har kuma da gidan Bwalili.

Hakkin mallakar hoto MaryAnn Ochota

Bwalili ce shugabar kauyen nasu, inda take jagorantar masu koyon sana'a da tsaftace muhalli da kula da yara, kuma suna taruwa duk ranar Lahadi domin su tattauna ayyukansu da yadda za su samu ci gaba, da kuma kara kwarin gwiwa.

Kauyen Bwalili na da kyakkyawan fata, ganin irin wahalar da suka sha a baya.

Akwai dai sauran rina a kaba, ganin yadda ake ganin shugaba Joseph Kabila zai soke zaben shugaban kasa bana, domin ya ci gaba da zaman-dirshan kan karagar mulki.

Ana kuma fargabar hakan na iya janyo wani sabon yakin da fararen hula za su dandana kudar su ta hanyoyin zamowa bayi da fuskantar fyade da yunwa da cin zarafi da rasa muhalli.