IMF ya dakatar da bai wa Mozambique kudi

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mai yiwuwa wasu kasashen su dakatar da tallafin da suke bai wa kasar.

Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF, ya dakatar da bai wa Mozambique kudi bayan ya gano cewa gwamnatin kasar ta ki bayyana basukan da ake binta na sama da dala biliyan daya.

Wani wakilin IMF ya ce mai yiwuwa ma wasu kasashen su ma su bi sahu wajen dakatar da tallafin da suke bai wa kasar.

Wannan dai zai sa matsi a kan Mozambique wadda ta dogara da tallafi daga kasashen waje domin tafiyar da kashi daya cikin hudu na kasafin kudinta.

Da ma kasar tana fuskantar matsalar tattalin arziki, domin haka ne ma haka Firai Ministan Mozambique ya tafi Amurka domin kokarin neman sulhu da manyan kasashen da ke ba su tallafi.