Trump da Clinton sun ci zaben fitar da gwani

Mutanen da ke son yi wa jam'iyyun Republican da Democrat takara a zaben shugaban kasar Amurka Donald Trump da Hillary Clinton sun lashe zaben fitar da gwani na New York.

Mr Donald Trump ya lashe zaben ne da fiye da kashi 60 cikin dari na kuri'un da aka kirga, inda ya kara bayar da tazara ga abokan takararsa Ted Cruz da John Kasich.

Ita ma Hillary Clinton ta yi wa abokin karawarta Bernie Sanders fintinkau inda ta lashe fiye da kashi 58 cikin dari na kuri'in da aka kirga.

A jawabinta, Mrs Clinton ta shaida wa masu goyon bayan abokin karawarta Sanders cewa akwai abubuwan da za su hada kawunansu fiye da wadanda za su raba kawunansu.

A jawabinsa na samun galaba, Mr Trump ya ce a bayyane take cewa an fitar da abokin fafatawarsa Senator Cruz daga tsayawa takarar shugaban kasar jam'iyar Republican.