Nigeria: Majalisar Wakilai za ta sayi motoci

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara lokacin da yake rantsuwar kama aiki.

Majalisar wakilan Najeriya ta ce ita ma za ta saya wa kowane daga cikin mambobinta su 360 mota ƙirar Peugeot 508, domin gudanar da ayyukan yau da kullum na majalisar.

Mai magana da yawun 'yan majalisar, Abdurrazak Namdaz, ya shaida wa BBC cewa za su karɓi motocin ne bashi daga kamfanin Peugeot a kan kuɗi Naira miliyan 10 kowacce.

Ya ce za su biya bashin ne wanda zai kasance fiye da naira biliyan uku a tsawon shekaru biyu.

Su ma dai takwarorinsu na majalisar dattawa su 109, sun sayi makamantan waɗannan motoci a kan fiye da Naira miliyan 35 kowaccensu.

Al'amarin dai da ya janyo kace-nace a ƙasar, har ma ƙungiyar ƙwadagon Najeriyar take barazanar ɗaukar mataki.