Obama na yin ziyara a Saudiyya

Hakkin mallakar hoto
Image caption Saudiyya dai tana fushi da Amurka cewa an juya mata baya

A ranar Laraba ne ake sa ran shugaban Amurka, Barack Obama zai kai ziyara kasar Saudiyya.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu take neman yin tsami a kan batun yaki da kungiyar IS da kuma shirin nukiliya na kasar Iran.

Shugaba Obama zai gana da Sarki Salman, sannan ya halarci wani taron koli na kasashen yankin Larabawa ranar Alhamis.

Wakilin BBC wanda yake a tawagar ta Shugaba Obama ya ce Saudiyya tana fushi da Amurka bisa tunanin cewa Amurkar ta juya mata baya musamman dangane da Iran.