BH: America za ta bayar da tallafin $40m

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kungiyar Boko Haram ta yi sanadiyar dubban mutane

Amurka ta ce za ta bayar da tallafin dala miliyan 40 ga kasashen tafkin Chadi da rikicin kungiyar boko Haram ya shafa.

A ranar Talata ne jakadiyar Amurka a Majalisar dinkin duniya, Samantha Power, ta yi wannan sanarwar.

Samantha ta kara da cewa tallafin zai taimaka wa mutane miliyan bakwai da 'yan kungiyar ta Boko Haram suka yi sanadiyar mutuwar kusan mutane dubu 15, ya daidaita.

Power ta ce wannan tallafin ya hada jimillar daukin da Amurka ta kai wa yankin tun shekarar 2014 zuwa dala miliyan 237.

Jakadar ta kai ziyara Kamaru, inda ta gana da Shugaba Paul Biya, kuma ta halarci wani taro da aka kona hauren giwa 2000 a wani yunkuri na ganin an kawo karshen farautar hauren giwa a kasar.