An tuhumi kamfanin Google

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Google zai iya fuskantar tara mai dimbin yawa.

Tarayyar Turai ta tuhumi kamfanin Google saboda aikata wasu abubuwa da suka karya ka'idojin yin gogayyar kasuwanci.

Lamarin ya faru ne a wata muhimmiyar jayayya mai nasaba da yadda kampanin ke tallata manhajarsa ta Android da ake amfani da ita a wayar salula.

Kwamishiniyar Tarayyar Turai kan harkokin yin gogayya, Margreth Vesteherr ta ce bincike ya nuna cewa abin da Google ya takaita yana dakile damar yin kirkira ta abokan gogayyarsa.

Google zai iya fuskantar tara mai dimbin yawa, a kuma tilasta masa ya bullo da sauye-sauye kan yadda yake gudanar da harkokin kasuwancinsa, idan aka kayar da shi a wannan shari'a.