Nigeria ta sa sharuddan zuwa aikin Hajji

Image caption Hukumar aikin hajjin Najeriya ta ce wadanda ba su taba zuwa hajji ba ne za su je bana

Hukumar aikin hajjin Najeriya ta ce wadanda ba su taba zuwa aikin Hajji ba ne za su samu damar zuwa aikin Hajjin bana.

Shugaban hukumar, Abdullahi Mukhtar , ya shaida wa BBC cewa sun dauki wannan matakin ne saboda karancin kujerun da ake fuskanta da kuma rashin kammala aikin fadada masallacin Harami.

A cewarsa, shekara biyu da ta gabata, lokacin da da gwamnatin Saudiya ta fara gyaran masallacin Harami, ta rage yawan mutanen da za su je aikin Hajji daga dukkan kasashen duniya kashi 20 cikin dari.

Sai dai shugaban hukamar ya ce a yayin da da suke sa ran za a janye wannan hukunci, gwamnatin Saudiya ta ce tana kara kokarin inganta masallacin Harami kuma dokar tana nan har yanzu.

Ga kuma karin bayanin da ya yi wa Raliya zubairu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti