Fashewar wani abu ta hallaka mutane 3 a Mexico

Mutane uku ne suka mutu, kana wasu da dama suka jikkata sakamakon fashewar wani abu, a wata matatar dangogin man fetur da ke kudu maso gabashin Mexico.

Fashewar dai ta tayar da wani bakin hayaki mai dauke da guba a wani gari da ke jihar Veracruz.

Gwamnan jihar, Javier Duarte ya ce an kwashe mutane fiye da dari zuwa asibiti.

An kuma kwashe wasu mutanen daga makarantu da wuraren sana'a.

Tuni jami'an gwamnati suka fara bincike kan musabbabin faruwar al'amarin.