An kashe masu aikin polio a Pakistan

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masu kai hare-hare na yin tarnaki wajen ganin an kawar da cutar a kasar.

'Yan sandan Pakistan sun ce wasu 'yan bindiga sun kashe jami'ansu bakwai da ke kula da masu yin allurar rigakafin cutar shan inna a birnin Karachi.

Sun ce an kashe 'yan sandan ne a hare-hare biyu daban-daban da aka kai musu.

Sai dai harin bai shafi masu aikin allurar polion ba.

Wadannan dai su ne hare-hare na baya bayan nan da ake kai wa masu bayar da allurar rigakafin polio a kasar.

Pakistan na cikin kasashe biyu da suka rage a duniya da ke fama da cutar ta shan inna.

Masu kai hare-hare na yin tarnaki wajen ganin an kawar da cutar a kasar.