Syria: Majalisar dinkin Duniya ta fara kwashe mutane

Garin Madaya na kasar Syria
Image caption Garin Madaya na kasar Syria

Majalisar Dinkin Duniya ta fara kwashe daruruwan marasa lafiya da wadanda suka jikkata da iyalansu daga garuruwan da aka yiwa kawanya a kasar Syria.

Mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniyar Stephane Dujarric ya ce wasu na bukatar agajin ceton rai da gaggawa.

Dakaru masu goyon bayan gwamnati ne suka toshe hanyoyin shiga biyu daga cikin garuruwan, Zabadani da Madaya.

Sauran garuruwan kamar al-Foua da Kefraya a Lardin Idlib kungiyoyin 'yan tawaye masu rike da makamai ne suka yi musu kawanya.

A bara ne bangarorin da ke fadan suka amince da yarjejeniya tsagaita wuta, amma ba a yi mata cikakkiyar aiwatarwa ba.