Burundi: Blatter ya so bai wa Nkurunziza aiki

Image caption Nkurunziza yana sha'awar kwallon kafa.

Tsohon shugaban Fifa Sepp Blatter ya ce jami'an gwamnatin Switzerland sun taba rokarsa ya kawo karshen rikicin siyasar Burundi ta hanyar bai wa Shugaba Pierre Nkurunziza aikin yi.

A sabon littafin da ya wallafa, Mr Blatter ya ce ya yi tayin bai wa Mr Nkurunziza - wanda ke da matukar sha'awar kwallo kafa - mukamin "jakadan kwallon kafa na Fifa" idan ya amince ya sauka daga mulki.

Mr Nkurunziza ya ki amincewa da tayin, kuma ya sake tsayawa takarar shugabancin Burundi a karo na uku, inda ya lashe zaben mai cike da cece-kuce.

Ma'aikatar harkokin wajen Switzerland ta tabbatar da cewa ta nemi taimakon Mr Blatter kan batun, ko da ya ke ta musanta cewa ta bukaci Mr Nkurunziza ya sauka daga mulki.

Wata sanarwa ta ce, "Abin da ya sa aka so ya karbi mukamin shi ne domin a tabbatar da zaman lafiya a kasar ta Burundi."

An yi wa Mr Nkurunziza wannan tayi ne a watan Mayu na shekarar da ta wuce, jim kadan bayan an fara zanga-zangar kyamar shirinsa na sake tsayawa takara.

Shugaban na Burundi yana matukar sha'awar kwallon kafa - yana da kungiyar kwallon kafa ta kansa mai suna Hallelujah FC, sannan ya taba zama kocin tagawar kwallon kafar kasar.