'Yan Boko Haram sun kashe mutum 11

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Boko Haram ta yi sandiyar mutuwar dubban mutane tun da ta fara kai hare-hare a shekarar 2009.

Kungiyar Boko Haram ta kashe mutane 11 sannan kuma mutane da dama sun jikkata a wani hari da ta kai kauyen Zango da ke jihar Yobe a arewa maso gabashin Najeriya.

Harin dai ya afku ne a daren ranar Talata, ko da yake ba a sani ba sai ranar Laraba, in ji Aisami Mamman wani dan kungiyar 'yan kato da gora.

Ya kara da cewa 'yan Boko Haram sun je kauyen cikin dare a kan dokuna suka fara harbe-harbe, abin da ya sa 'yan kauyen suka arce cikin daji.

Sai dai 'yan kungiyar ta Boko Haram sun bi su har cikin dajin suna harbe su, sannan daga bisani suka cinnawa kauyen wuta.

Harin dai ya zo ne mako biyu bayan wani hari mai kama da wannan a wasu kauyuka biyu da ke kusa da kauyen na Zango ya yi sanadiyar mutuwar mutum ashirin.