Za a halasta shan tabar wiwi a Canada

Ministar lafiyar Canada ta ce gwamantin kasar za ta zartar da dokar da za ta halasta sayar da ganyen wiwi.

Idan aka zartar da dokar, za ta sa Canada ta zama kasa mafi girma a kasashen Turai da za ta halasta amfani da wiwi.

A ranar Laraba ne dai Ministar lafiya, Jane Philpot, ta sha alwashin tabbatarwa cewa yara ba su samu tabar wiwi ba.

Firai Minista Justin Trudea ya sha alwashin zartar da dokar a lokacin da yake yakin neman zabe.

Sanarwar ta zo dai dai ne da ranar 20 ga watan Afrilu - wacce rana ce ta hutu ga masu goyon bayan shan tabar wiwi.

Daruruwan masu amfani da ganyen wiwi sun yi zanga-zanga a wajen majalisar dokokin kasar da ke Ottawa a ranar Laraba.

An halasta yin amfani da ganyen wiwi a matsayin magani a Canada.

Wasu sun ce halasta shan wiwi zai ragewa ma'aikatar shari'ar kasar wahala.

Ms Philpot ta ce "Za mu yi aiki tare da jami'an tsaro domin su karfafa gwiwa wajen samar da matakan shari'ar wadanda suka dace. Mun san ba zai yiwu mu iya shawo kan matsalar ba."

Duk da haka, Gerard Deltel, wani dan majalisa da ke jami'yyar 'yan adawa ta Conservatives yana adawa da dokar, inda ya ce za ta cutar da lafiyar mutanen Canada.

Ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na Reuters cewa, halasta shan ganyen wiwi, shi ne abu mafi muni da za a yi wa matasan Canada.

Mr Trudeau ya nada Bill Blair, tsohon shugaban 'yan sanda a Toronto, babban birnin Canada, a matsayin mai kula da harkokin doka kan batun.

Mista Blair ya ce "za mu sanya ido kan wanda aka sayarwa da wiwi da wanda ya saya da kuma lokacin da aka sayar da kuma yadda ake amfani da ita".

A Amurka, masu kada kuri'a a jihohi guda hudu da kuma gundumar Columbia sun riga sun halasta amfani da tabar wiwi a wasu wurare.