Nigeria: Kun san yadda za a warware matsalar fetur?

Image caption 'Yan bunburutu na cin kasuwa a Abuja, babban birnin Najeriya

Masana kan albarkatun kasa a Najeriya sun soki matakan da gwamnatin kasar ta dauka na shawo kan matsalar karanci da tsadar man fetur da ta dade tana addabar al'umma.

A ranar Laraba ne dai karamin ministan man kasar, Ibe Kachikwu, ya ce mai zai wadata sakamakon shigo da man da gwamnatin kasar ta yi, sannan ta fara rarraba shi zuwa yankunan kasar.

Sai dai masanan sun ce duk wani kokarin daukar matakan wucin-gadi da gwamnatin ke yi, kamar kashe maciji ne ba a sare kansa ba.

Masanan sun ce idan dai har ba a gyara rumbunan adana mai da ke fadin kasar ba to babu wani tasiri da shigo da mai daga kasashen waje zai yi.

Sauran hanyoyin shawo kan matsalar da masanan suka shimfida su ne cire hannun gwamnati daga tace man da rarrabashi da kuma sayar da shi.

Sannan kuma gwamnati ta bar kasuwarsa man a bude kamar yadda aka yi wa kasuwar hanyar sadarwa a kasar.