Ana goge hotunan fyaɗe daga intanet

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Yaran da hotunansu suka cika intanet 'yan shekara 10 ne zuwa kasa

Wata kungiya mai hana cin zarafin kananan yara ta Birtaniya, ta ce an goge kimanin shafuka da ke nuna irin yadda ake cin zarafin yara kanana mai alaka da jima'i, guda 70,000 da aka gano a kan intanet, a bara.

A 2014 ne dai aka ba wa gidauniya mai sanya ido kan abubuwan da ke gudana a kafar intanet wato IWF damar nemo hotunan da kuma yanke hukuncin yadda ya kamata a yi da su.

Abubuwan kuma da gidauniyar ta samu sun hada da hotuna masu motsi da sandararru guda 1,788 na yaran da aka watsa masu shekaru biyu da kasa da haka.

Da take bayar da rahoto kan ayyukanta a 2015, gidauniyar da IWF ta ce:

Hakkin mallakar hoto THINKSTOCK
Image caption Hotunan fyade ne suka fi yawa a kan intanet

An gano rahotanni 68,092 da suke dauke da hotunan jima'i da yara wadanda ba su halatta ba.

An yi kiyasin cewa kaso 69 cikin 100 na yaran da aka watsa 'yan shekara 10 ne zuwa kasa.

Kaso 34 na hotunan sun kunshi yaran da aka yi wa fyade ne.

Shugabar gidauniyar IWF, Susie Hargreaves, ta ce " Binciken da muka yi bara ya samar da bayanan da ba taba samun irinsu ba."