An kai samame a ofishin Mitsubishi

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jamai'an kamfanin sun nemi gafarar masu mu'amala da su.

Jami'ai a kasar Japan sun kai samame a ofishin kamfanin kera motoci na Mitsubishi bayan kamfanin ya amincewa cewa ya yi karya a bayanan da ya bayar na yawan man da motocin ke sha.

Jami'an sun gudanar da bincike a cikin kamfanin da ke birnin Okazaki.

Mitsubishi ya amince cewa ma'aikatansa sun sauya bayanan na'urar da ke kididdigar gudu a fiye da motoci 600,000.

Kakakin gwamnatin kasar ya ce suna daukar lamarin a matsayin abu mai matukar muhimmanci, yana mai cewa an bukaci kamfani ya mika rahoto kan yadda yake gudanar da ayyukansa.

An bai wa kamfanin zuwa ranar 27 ga watan Afrilu domin ya mika rahoton nasa.