Amurka ta yi doka kan jirage marasa matuƙa

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jirgi mara matuki

'Yan siyasa a Amurka suna duba yiwuwar sabuwar doka da zai ba wa hukumomi damar tsayar ko kuma kakkaɓo da jirage marasa matuka, a duk lokacin da raɓi filin jirgin sama.

A ranar Talata ne dai majalisar dattawan Amurka ta amince da matakin wanda wani ɓangare ne na ƙudirin dokokin harkokin sufurin jirgin sama.

Kuma sun yi haka ne sakamakon yawan ƙorafin da suke samu kan jirage marasa matuƙa, bayan wani taho mu-gama da wani jirgi mara matuƙi ya yi da jirgin sama mallakar kamfanin British Airways a kusa da filin jirgin saman Heathrow da ke London.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Jirgi mara matuki ya yi taho mu gama da jirgin sama

Dokokin dai za su iya bayar da damar yin amfani da jirage marasa matuƙa wajen yin safarar mutane.

Sanata Bill Nelson na jam'iyyar Democrat wanda yake wakiltar Florida, ne ya fito da waɗannan matakan kiyaye haɗurra.

Ya kuma yi gargaɗin cewa jirgi marar matuƙi da ya antaya cikin injin jirigin sama zai iya sanya jirgin ya tsaya da aiki ko kuma ya yi bindiga.

ƙudirin dokar yana kuma ɗauke da sabbin dokoki da za su tabbatar da jiragen sama sun ɗauki matakan kariya daga mutanen da ka iya juya akalar jirgi daga nesa.

Yanzu haka, ƙudirin dokar zai je ga majalisar wakilai domin duba yiwuwar tabbatar da shi ya zamo doka.