Chad: Deby ya lashe zabe a karo na biyar

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Idris Derby ya fara mulkin Chadi a shekarar 1990.

Shugaban kasar Chadi, Idriss Deby, ya sake lashe zaben shugaban kasar a karo na biyar bayan ya samu fiye da kashi 60 na kuri'un da aka kada a zagayen farko na zaben.

Idriss Deby ya fara shugabancin kasar a shekarar 1990, lokacin da ya yi wa gwamnatin wancan lokacin juyin mulki.

Dan takarar babbar jam'iyyar hamayya, Saleh Kebzabo ne ya zo na biyu, inda ya samu kashi 13 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Da ma dai 'yan hamayya sun ce ba za a yi musu adalci a zaben ba.

Kasar ta Chadi ce ta bayar da sansanin dakarun gamayyar tsaro na kasashe biyar da ke yaki da kungiyar Boko Haram.