Yarjejeniya kan sauyin yanayi

Hakkin mallakar hoto AFP

Wakilai daga kasashe 170 za su sanya hannu a kan wata yarjejeniya da aka tsara a birnin Paris, game da takaita sauyin yanayi, a wani taron Majalisar Dinkin Duniya da ake gudanarwa a New York da ke Amurka.

Majalisar Dinkin Duniya na fatan samun sakamako a ranar farkon sanya hannun zai bai wa kasashe kwarin gwiwar tunkarar Majalisun dokokinsu, inda zai bude hanyoyin tabbatar da yarjejeniyar kamar yadda aka sa rai.

Dole ne akalla kasashe 55 da ke fitar da kashi 55 cikin dari na gurbatacciyar iska a duniya, su amince kafin yarjejeniyar ta fara aiki.

Kasashen Amurka da China, biyu daga cikin kasashen da suka fi gurbata muhalli a duniya, sun ce za su yi kokarin rage iska mai gurbata muhallin.

Yarjejeniyar dai za ta tabbatar da cewa kasashen sun kimanta irin hayaki mai guba da suke fitarwa, musamma sinadarin Carbondioxide da sauransu.

Za a bai wa kasashen da ba su sanya hannu a yarjejeniyar ba a ranar Jumma'a, ratar shekarar guda domin su yi hakan.