Indiya: Sadakin bakar mace ya fi yawa

Hakkin mallakar hoto unk

Wata mata 'ya kasar India ta bayyana kin amincewar ta ta auri wani yaro da iyalinsa suka bukaci ta biya kudin sadaki mai yawa, saboda ita bakar fata ce.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook, matar mai suna Jyoti Choudhary ta ce ta ki amincewa ta biya kudin da aka nema saboda launin fatar ta.

Ta ce hakan na nuni da cewa al'ummar Jamshedpur da ke gabashin India har yanzu ba su waye ba.

Ita dai Ms Choudry wadda Injiniya ce, ta ce ba za ta samu matsalar samun wani mijin ba.