Kenya: An sa hannu kan dokar hana shan kwayoyi

Hakkin mallakar hoto

Shugaban kasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ya sa hannu kan dokar hana shan kwayoyin kara kuzari, wadda ta bude hanya ga kasar ta shiga gasar wasannin Olympics na wannan shekarar.

An yi ta fargabar cewa mai yiwuwa 'yan wasan Kenya ba za su shiga gasar ta bana ba da za a yi a Rio ba, bayan da kasar ta gaza cika ka'idoji biyu da hukumar yaki da shan kwayoyi masu kara kuzari ta duniya ta bayar.

Hukumar ta ce matakan da Kenya ke dauka a baya ba su cika ka'idojinta ba.

An hana 'yan wasan Kenya da dama shiga gasar saboda shan kwayoyin masu kara kuzari.