Yunkurin samar da hadin kai a Libya

Tsayin ciyayi a wasu wuraren na Bab al-Aziziya ya kai gwiwoyin mutane da ke yankin da ke tasowa a wajen garin Tripoli inda ake zargin Kanar Muammar Gaddafi ya ci zarafin 'yan kasarsa.

Shekara biyar kenan da dakarun Nato suka yi ruwan bama-bamai a kan fadarsa da wani wurin wasan yara da kuma shelikwatar jami'an tsaro.

Tun daga lokacin aka yi watsi da wajen, wasu ma suka ce har ma Libya.

Amma yanzu, al'ummar kasashen waje suna saka ido a kan kasar.

'Yan kungiyar IS suna zaune a garin Sirte, mahaifar marigayi Gaddafi, kuma 'yan gudun hijira da dama suna barin Libyar zuwa Turai.

Yanzu kuma makomar Libyar ta zama muhimmin abu ga Turai.

Mataimakin firai minista Mousa al-Koni ya ce an fuskanci kalubale wajen shiga babban birnin kasar a watan Mayu, yana mai cewa, "amma kuma mun godewa Allah da kuma sojijin ruwa na Amurka, mun samu mun yi aikin kuma mu ka shiga Tripoli"

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Magoya bayan gwamnatin Libya sun gudanar da zanga-zanga a Tripoli babban birnin kasar, a farkon wannan watan.

Gwamnatin da ke cike da kwarin gwiwa tana aiki ne daga sansanonin sojin ruwa mai tsaro sosai.

Tana samun goyon bayan majalisar dinkin duniya amma ita ma tana da masu adawa.

Akwai wasu gwamnatocin biyu a Libyar inda kungiyar da ke fafutikar kafa daular musulinci ke jagoranta da kuma gwamnatin da majalisar dinkin duniya ke jagoranta a Tobruk a gabashin kasar.

Sannan kuma akwai sojojin sa kai da dama. Ba su da niyyar barin a kwace yankinsu.

"Muna fuskantar kalubale da dama wajen kwace ma'aiktu da kuma wuraren da sojojin sa kai su zaune da kuma mayar da 'yan sanda da sojojin bakin aikinsu, in ji Mista Koni. "Sun fara gudanar da aikace-aikacensu kuma sun kwace ikon wasu titunan da gine-gine. Muna da kyakkyawar fata sosai."

'Muna son gwamnati daya'

Mun bi wasu sojojin sa-kai na Nawasi sintiri da suke yi da daddare a kan hanyar da ke kusa da teku a birnin Tripoli.

Wasu mutane masu dauke da mugayen makamai sanye da kayan sojoji sunyi jerin gwano. Ya yi kama da aikin sintiri da 'yan sanda suka saba yi.

Sojojin sa-kai na Nawasi suna aiki tare da ma'aikatar cikin gida ta Libya amma kuma sojojin sa-kai da dama suna yin gaban kansu.

Kasa da kashi 50 cikin 100 suna bin doka, in ji Hussam Mohammed, mai magana da yawun ma'aikatar cikin gida na kudancin Tripoli.

Ya amince cewa sojojin sa-kai 10 ne aka bai wa horo kuma aka saka su a cikin ma'aikatar.

Ya kira da a hada kai, kamar sauran mutanen kasar.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Fayez Seraj, shugaban gwamnatin hadakar ya gana da magoya baya a wani masallaci a Tripoli.

Adel Kakli ya dade yana jira a samu sabuwar gwamnatin Libya.

Ya shafe shekara 17 a birnin Manchester kafin ya koma gida a shekarar 2011 domin yakar Kanar Gaddafi.

Ya ba da ra'ayinsa a kan sabuwar gwamnati a wani wurin shakatawa da ke kusa da teku.

Ya ce ba za su "yi wa mutane abubuwan da suke so ba amma za su saka mu a kan hanya.

"Mun gani a fuskokin wadanda suke murmushi. Sun yi farin cikin zuwan gwamnatin."

Ga Mista Kakli, rikicin da aka yi shekara biyar da suka wuce ba wani abin mamaki ba ne.

Ya kara da cewar "Mutane da dama ba su ji dadi ba amma a gare ni ba sabon abu ba ne idan aka yi juyin juya hali".