'An mare ni domin ni mace ce'

Image caption Ba a san ranar da Mr Ekpend zai je gaban 'yan majalisar ba.

Majalisar wakilan Najeriya ta umarci shugaban hukumar da ke kula da gidajen yarin kasar ya bayyana a gabanta bayan an zargi jami'an da ke kare lafiyarsa da marin wata 'yar majalisa.

Onyemaechi Mrakpor mai shekaru 49 ta shaida wa BBC cewa an diran mata ne a dalilin cewa ta sha gaban ayarin motocin shugaban hukumar da ke kula da gidajen yarinPeter Ezenwa Ekpendu a ranar Laraba.

A cewar Misis Mrakpor, "Na dauka cewa wani hadari ne aka samu wani ya bugi motar wani. Saboda haka na sauke gilashin motata." Ta kara da cewa,

"Yin hakan ke da wuya sai wasu mutane maza cikin kayan sarki na jami'an gidajen yari, suka sauko daga motarsu ita ma mallakar hukumar gidajen yari; sai na cewa wanda ya zo ta inda nake zaune me yake faruwa? Me yasa kake bubbugar motata? Sai kawai na ji mari fau!"

Lamarin ya harkuza masu kula da lafiyarsa, inda suka tare ta, kana suka yi ta marinta, a kan idanun Mr Ekpendu a harabar majalisar dokokin.

Wani dan majalisa ya ce Mrs Mrakpor ta yi ta kuka a lokacin da take bayar da labarin abin da ya afku.

Sai dai Francis Enobore, mai magana da yawun shugaban hukumar kula da gidajen yarin, ya musanta cewa jami'an hukumar sun ci zarafin 'yar majalisar wakilan.

"Na tausayawa mata a Najeriya. Domin sai da suka fahimci ni mace ce sannan suka fara zagi na." In ji Mrakpor.

Mrs Mrakpor ta ce lamarin ya razana ta, kuma ya kunyata ta, don haka ta shigar vda kara wajen 'yan sanda.