An kashe wani Farfesa a Bangladesh

Image caption Ana yawan samun kashe wadanda suka shahara a wani fanni a Bangladesh

An kashe wani Farfesan jami'a a Bangladesh wanda ake zargin masu kaifin kishin Islama ne suka kashe shi.

'Yan sanda a arewa maso yammacin birnin Rajshahi sun ce Rezaul Karim Siddique wanda farfesa ne a bangaren ingilishi an kai masa harin ne da adduna a lokacin da yake jiran mota zai tafi aiki.

'Yan uwansa sun ce shi ne editor mujallar Literary, sannan kuma shi ne ya kirkiri wata makarantar koyar da kade-kade da wake-wake.

Ana dai yawan samun kashe wadanda suka shahara a wani bangare a Bangladesh, sai dai kuma wani abokin aikin farfesan ya ce bai taba yin rubutu ko wata magana marar dadi game da addini ba.