Darfur: Sakamakon kuri'ar raba gardama

Hukumar zaben Sudan ta ce kashi 97 cikin dari na kuri'un da aka kada a zaben raba gardamar da aka gudanar a kan matsayin yankin Darfur ya nuna rinjayen goyon bayan ci gaba da kasancewar yankin kan matsayin da yake a yanzu.

An bada zabi ne tsakanin cigaba da wanzuwar jihohi biyar da ake da su a yanzu ko kuma hade su a matsayin jiha guda daya.

Sai dai manyan kungiyoyin yan tawaye da na adawa wadanda ke bukatar karin yancin cin gashin kai sun kauracewa zaben.

Kuri'ar rana gardamar na daga cikin shirin zaman lafiya da aka cimma domin kawo karshen tashe tashen hankula da aka shafe shekaru 13 ana yi wanda kuma ya hallaka mutane kusan dubu 300 da kuma wasu miliyoyin jama'a da suka rasa muhallansu.