Ina Abubakar Shekau yake?

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter

Yayin da rundunonin sojin sama da na kasa na Najeriya suke ikrarin sun kusa karya lagon kungiyar Boko Haram, mutane da dama na neman sanin hakikanin inda jagoran kungiyar, Abubakar Shekau, yake.

A baya dai rahotanni sun sha nuna cewa jami'an tsaro sun hallaka jagoran na Boko Haram, Abubakar Shekau amma kuma sai a gan shi ya fito a faifan bidiyo yana yin raddi.

Ko a watan da ya gabata ma sai da Shekau din ya fito a wani bidiyo, duk da cewa yana da alamun gajiya a tare da shi.

Sai dai babban Hafsan sojin saman Najeriya, Air Marshall Sadique Abubakar ya shaidawa BBC cewa wurin da Shekau yake ba shi ne abin da suka fi ba wa mahimmanci ba, illa iyaka dai ganin sun murkushe kungiyar.

Ya kuma ce rundunonin sojin kasar sun yi nasara wajen tarwatsa kungiyar.