Gwamatin Najeriya ta tsoma baki cikin rikicin Arik air

kamfanin jiragen sama na Arik Hakkin mallakar hoto BOEING MEDIA
Image caption Jirgin saman kamfanin Arik

Gwamnatin Najeriya ta tsoma baki cikin takaddamar da ta kaure tsakanin kamfanin ARIK da kuma kungiyoyin ma'aikatan sufurin jiragen sama kan bashin naira biliyan 12 da kungiyoyin suka ce suna binsa.

A ranar Laraba ne wakilan kungiyoyin suka hana jiragen kamfanin tashi daga filin jirgin saman Legas babban birnin kasuwanci na kasar kan saboda wannan bashin.

Kasancewar kamfanin ya musanta zargin kungiyoyi na zama turun bashi, ministan sufurin kasar Hadi Sirika ya shaidawa BBC cewa sun shiga tsakani domin kawo maslaha.

Ta ce idan har ta tabbatar da gaskiyar lamarin , za ta tilastawa kamfanin akan ya biya ma'aikatan hakokkinsu.