Papa Wemba ya rasu

Papa Wemba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Marigayi Papa Wemba a lokacin da ya ke wasa

Shahararen mawakin nan dan kasar Congo, Papa Wemba ya rasu bayan da ya fadi ya yinda ya ke wasa a kasar Ivory Coast.

Kakakin mawakin ya ce Mista Wemba ya rasu ne a wani asibiti da ke birnin Abidjan kuma shekarunsa 66 a duniya.

Papa Wemba wanda asalin sunansa Jules Shungu Webadio ya kawo sauyi a fanin wake wake na kasar Congo a shekarun 1970 da kuma 1980,kuma ya sa salon wakarsa da aka yi wa lakabi da Soukous ya samu karbuwa sosai a nahiyar Afrika.

Sai dai a baya ya aiwatar da wasu abubuwa da suka janyo cece-ku-ce, kamar lokacin da aka tsare shi a Zaire bisa zargin neman diyyar wani janarar.

Haka kuma shekaru 13 da suka wuce an yanke ma sai hukunci zama a gidan kaso a Belguim har na tsawon lokaci bayan da aka same shi da laifin safarar mutane.