Buhari ya bukaci a raba kayan abinci

Image caption Shugaba Buhari ya ce 'yan Najeriya sun fada cikin talauci ne saboda rashin tsari na gwamnatocin da suka wuce.

Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin a fitar da abinci tan 10,000 daga rumbun ajiyar abinci na kasa domin raba wa 'yan kasar a yunkurinsa na saukaka wa jama'a tsadar kayan abinci da ake fuskanta.

Shugaba Buhari ya kuma bayar da umarni ga ma'aikatar aikin gona ta tallafa wa masu jini a jika; maza da mata da ke zaune a sansanonin 'yan gudun hijira su koma gona domin a haɓaka samar da abinci.

Wata sanarwa da ke dauke da sa hannun kakakin shugaban Najeriyar, Malam Garba Shehu ta kuma ce, shugaban Nigeriyar yana ɗaukar matakai na ganin cewa jama'a sun samu sauƙin rayuwa.

Gwamnatin Najeriyar ta kuma ce halin da jama'a suke ciki yanzu sakamako ne na rashin shiri domin gobe, cin hanci da rashawa, da kuma rikicin Boko Haram.

'Koyar da sana'a'

Shugaba Buhari ya kara da cewa gwamnati tana daukar matakai na sauƙaƙawa jama'a kuncin rayuwa, wadanda suka hada da samar da tallafin N5000 ga mutanen da ba su da galihu.

Gwamnatin Najeriyar ta ce akwai wani shiri na daukar matasa masu shaidar karatun digiri 500,000 aikin koyarwa na sa-kai, inda gwamnatin tarayya za ta rika biyansu yayin da suke ci gaba da neman aiki.

Akwai kuma wani shiri na koyar da sana'a ga matasa 370,000, kuma za a rika biyansu yayin da suke koyon sanao'i.