Sule Lamido zai nemi shugabancin Najeriya

Tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, Alhaji Sule Lamido, ya ce zai yi takarar shugabancin kasar a shekarar 2019.

Wata majiya ta kusa da gwamnan ta shaida wa BBC cewa tsohon gwamnan zai tsaya takara idan jam'iyyarsa ta PDP ta ba shi dama.

Da ma dai wasu rahotanni daga kasar sun ambato Alhaji Sule Lamido yana cewa zai tsaya takarar shugabancin na Najeriya.

Tsohon gwamnan dai yana cikin mutanen da suka kafa jam'iyyar PDP, wacce ta sha kaye a zaben shekarar 2015, bayan ta kwashe shekara 16 tana mulkin Najeriya.

Kazalika, Alhaji Sule Lamido yana cikin gwamnonin PDP da a kafin zaben 2015 suka balle daga jam'iyyar ta PDP, suka kafa abin da suka kira 'sabuwar PDP', lamarin da ya sa da dama daga cikinsu suka koma jam'iyyar APC, ko da ya ke Alhaji Sule Lamido ya ki binsu cikin jam'iyyar.

Hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa a Najeriya ta gurfanar da Alhaji Sule Lamido da wasu 'ya'yansa bisa zargin sace makudan kudade.