Ngugi: An fassara labarinsa zuwa harsuna 30

Wata mujallar adabi ta Internet Jalada ta ce, an fassara wani labari da fitaccen marubucin nan dan kasar Kenya Ngugi wa Thiong'o ya rubuta zuwa harsunan Afirka 30.

Mujallar ta ce wannan shi ne gajerin labari da yafi kowanne samun fassara zuwa harsuna da dama.

An fassarar labarin ne zuwa harsunan da suka haɗa da Amharic, Larabci, Lugunda, Swahili, Hausa, Igbo, Ibibio, Ewe, Rukiga, Zulu, da sauransu.

Mujallar Jalada wadda ta haɗa wasu marubuta 'yan Afirka ta ce, manufar fassara wannan labari zuwa harsunan Afirka shi ne, baiwa 'yan Afirka damar fahimtar juna ta hanyar adabi.

Asalin labarin dai Ngugi wa Thing'o ya rubuta shi ne da harshensa na Kikuyu, wanda ɗaya daga cikin manyan harsuna ne a Kenya.

Marubucin shi da kansa ya fassara labarin zuwa Turanci.

Sunan labarin da harshen Kikuyu shi ne, 'Ituĩka Rĩa Mũrũngarũ: Kana Kĩrĩa Gĩtũmaga Andũ Mathiĩ Marũngiĩ'

An fassara sunan labarin zuwa Hausa inda aka kira shi, 'Yadda Mutum Ya Fara Tafiya A Tsaye'

Ngugi wa Thing'o marubuci ne da yayi fice wajen ƙarfafa 'yan Afirka su rika yin rubutu cikin harshensu.