Saudiyya za ta rage dogaro da fetur

Hakkin mallakar hoto
Image caption Kudaden shigar Saudi Arabia na zuwa ne daga mai yanzu

Gwamnatin Saudiyya ta amince da wasu shirye shirye na fadada hanyoyin samun kudaden shigar ta, ba tare da ci gaba da dogaro da kudaden man fetur ba.

Kusan kashi 80 cikin 100 na kudaden shigar kasar na zuwa ne daga man fetur, sai dai farashinsa na ci gaba da faduwa tun daga shekarar da ta gabata.

Karkashin shirin, kasar ta na hasashen abin da zai faru a shekarar 2030, inda za a sayar da kasa da kashi biyar na hannayen jarin kamfanin man kasar na Aramco .

A jawabin sa ta gidan talabiji, mataimakin Yarima mai jiran-gado Mohammed bin Salman ya ce an sanya kamfanin a kasuwa inda za a sayar da shi kan $2.5tn

Yarima Mohammed ya ce za a yi amfani da bangaren kudaden da za a samu daga hannayen jarin kamfanin domin kirkirar wani sabon asusun ajiya don gobe na $2.5tn

Ana tsammanin a ranar Litinin za a fitar da karin cikakkun bayanai game hasashen abin da zai faru a kasar nan da shekara 2030

A wata hira da kafar yada labarai ta Bloomberg a makon da ya gabata, Yarima Mohammed ya ce za a iya kirkirar haraji daga kayayyakin kawa da kuma lemunan zaki.

Sai dai ya ceshirin ba zai cutar da talakawan kasar ba